News
Trending

Me ya sa ake wahalar ruwan sha a cikin birnin Kano?

Al’ummar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, musamman cikin birnin jihar ana fuskantar matsalar karancin ruwa sha, lamarin da ke tilastawa magidanta sayen ruwa daga masu tura kurar ruwa.

Magidantan na ci gaba da kokawa kan tsadar ruwan shan da masu kurar ruwa ke sayarwa, inda a yanzu farashin kowacce jarka daya yake kamawa daga naira 100 zuwa 150.

Unguwanni da dama suna fama da matsalar ruwan, inda wasu suka shafe lokaci mai tsawo ba tare da samun ruwan fanfo ba.

Ga alama a iya cewa jama’a a cikin birnin Kano sun shiga halin rashin tabbas saboda yadda ruwan sha ke neman ya gagaresu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button