
Tunda fari dai tsohon Gwamnan Kadunan, Malam Nasir El-Rufai, na tsare ne a Hukumar EFCC tun daga ranar Litinin bisa zargin cin hanci da rashawa, yanzu kuma zai fuskanci tuhume-tuhumen aikata laifukan yanar gizo daga Hukumar Tsaron Farin Kaya (SSS).
A daren yau Laraba ne SSS ta cafke tsohon gwamnan lokaci kadan bayan Hukumar EFCC ta sake shi.
Tun daga ranar Litinin EFCC ke tsare da shi kan zargin cin hanci da rashawa.
An ba shi beli da misalin karfe 8 na dare a ranar Laraba, amma nan take jami’an SSS suka sake kama shi, inda aka ce sun yi masa kwanton bauna a harabar hedikwatar EFCC, a cewar wasu shaidun Jaridar Premium Times.
An danganta kama shi da SSS ta yi da zargin cewa ya yi kutse ba bisa ka’ida ba cikin sadarwar wayar Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan Harkokin Tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu.




