
Matasa na barazanar fara tattakin mutum miliyan 1 a Abuja kan ci gaba da tsare El-rufai
Zanga-zanga ta ɓarke a wasu sassan Jihar Kaduna kan ci gaba da tsare tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai, inda matasa suka nemi a sake shi nan take.
Masu zanga-zangar sun ce tsare shi duk da shari’ar da ke gaban kotu na tayar da tambayoyi kan bin doka, tare da barazanar shirya tattakin mutum miliyan ɗaya a Abuja idan ba a sake shi ba.
Wasu ‘yan adawa sun danganta lamarin da abin da suka kira takura wa muryoyin adawa, suna mai cewa har da kama tsohon AGF, Abubakar Malami.
Zanga-zangar ta zo ne yayin da jami’an DSS suka gaza gabatar da shi a kotu kan zargin laifukan yanar gizo.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito an gudanar da zanga-zangar a Kaduna da Kafanchan cikin lumana, ba tare da rahoton tashin hankali ba.



