News
Trending

Zaa iya garkameni nan bada dadewa ba. – ElRufa’i

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam’iyyar hamayya ta ADC ya yi zargin cewa dole ne ta sa wasu yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki ko kuma ci gaba da zama a cikinta.

Gwamnan na yin wannan zargi ne yayin da hada-hadar siyasa ke neman ɗaukar harama gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.

A baya-bayan nan El-Rufa’i ya tsananta sukar da yake yi wa gwamnatin shugaban Najeriya Bola Tinubu da kuma jam’iyyar APC mai mulki, wadda a ƙarƙashinta ne ya yi gwamnan jihar Kaduna na shekara takwas.

A wata tattaunawa da BBC, El-Rufa’i ya ce duk da cewa ba a riga an kama shi ba, amma an kama na kusa da shi, kuma yana tunanin za a iya zuwa kansa nan ba da daɗewa ba.

“An kama mutum wajen guda huɗu waɗanda muka yi aiki da su a Kaduna, saboda haka ni ma lokaci ne, ni ma za a neme ni,” in ji El-Rufa’i a tattaunawar tasa da BBC.

A baya-bayan nan kame da kuma shari’ar da ake yi wa tsohon ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami sun ɗauki hankali, inda har yanzu yake riƙe a hannun hukuma.

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta ƙasar EFCC ta zargi Malami da laifukan da suka haɗa da amfani da muƙami ba bisa ƙa’ida da kuma safarar haramtattun kuɗade.

Haka nan daga baya an sake kama shi inda hukumomin ƙasar ke tuhumar sa da ayyukan tallafa wa ta’addanci.

Malami, wanda ake kallo a matsayin jigo a tafiyar ƴan adawar shugaba Bola Tinubu a Najeriya ya musanta zarge-zargen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button