
Musulmai da ke ibada a Masallacin Jamie Usmania na birnin Bradford a ƙasar Birtaniya sun rungumi motsa jiki gadan-gadan domin samun kuzarin yin ibada cikin annashuwa.
A kowane mako bayan sallar azahar, musulman da galibinsu shekarunsu suka kama daga 50 zuwa 80 sukan motsa jiki na aƙalla minti 45.
Suna yin salo daban-daban na motsa jiki, kuma bayan sun gama su yi hira suna shan shayi da tauna biskit da kuma ‘ya’yan itatuwa domin ƙarfafa zumunta.
A kwanakin baya ne bidiyon motsa jikinsu da aka wallafa a shafin zumunta na masallacin ya karaɗe shafukan intanet inda, abin da ya sa aka riƙa kira ga masu kula da masallacin su aiwatar da irin wannan tsarin a duka faɗin Birtaniya da kuma ƙasashen Malaysia da Canada.
Kazalika ana sa rai za a bayar da irin wannan dama ga mata da ƙananan yara.




