News

‘Yadda aka kashe rabin ƙawayena a harin bam kan makarantarmu’

Ranar ta kasance kamar kowace rana ga tagwaye Makarem da Ikram, ‘yan shekara 18, a lokacin da aka kai wa makarantarsu harin bam a Sudan.

Makarem ta kasance tana cikin ajin Turanci yayin da Ikram take cikin ajin kimiyya, lokacin da suka ji wani “ƙara da ba mu saba ji ba” daga wajen makarantar.

Ashe harin bam ne ya auka wa makarantar.

Makarem ta bayyana cewa ta samu rauni a kafadarta lokacin harin, yayin da abokan karatunta da ke fikin ajin suka kwanta a ƙasa domin tsira, dukkaninsu suna ta ihu.

“Mun raɓe a gefen bango, inda wata daliba da ke tsaye a gabana ta sanya hannu a kafadarta ta ce, “Kafadarki na zubar da jini.”

A cikin wannan rikici, ‘yan biyun waɗanda ke a ajujuwa daban-daban, suka yi ƙoƙarin haɗuwa amma ba su yi nasara ba. Daga baya, Ikram ta fara neman Makarem ba tare da ta sani cewa an riga an kai ta asibiti ba.

Kamar sauran waɗanda suka jikkata, mazauna garin ne suka kai Makarem asibiti, waɗanda suka yi amfani da motoci da keken doki saboda babu motocin daukar marasa lafiya a birnin el-Obeid.

Daga bisani dai malamai da abokan ajin Makarem suka shawo kan Ikram da ta daina neman ‘yar uwarta ta koma gida.

Sai da Makarem ta koma gida daga asibiti a ranar ne iyalanta suka gane cewa tana raye.

Ikram ta ce, “Na tsaya a wajen ƙofar gida ina jira na ga ko za ta dawo, a lokacin da na gan ta tana zuwa, kawai duka muka fashe da kuka.”

Ikram dai ba ta ji rauni ba saboda tana cikin ɓangaren makarantar da harin bam ɗin bai yi wa illa ba.

Harin ya yi sanadiyyar mutuwar malamin Turancin Makarem da Ikram da wasu ɗalibai 13 yayin da da dama suka jikkata a harin bam ɗin da aka kai makarantar ta Abu Sitta, da ke el-Obeid ta jihar Kordofan ta Arewa, a watan Agustan 2024.

Makarantar na da ɗalibai aƙalla kimanin 300.

Hukumomin yankin sun zargi dakarun RSF da ke yaƙi da rundunar sojin Sudan da kai harin bam ɗin.

RSF ba ta yi wani bayani kan wannan lamari ba kuma ba ta amsa buƙatar BBC ta yin tsokaci ba saboda ba a tabbatar ko harbin bam ɗin a makarantar da gangan aka kai shi ba.

Makarem ta ce an kashe rabin abokan karatunta a harin yayin da sauran rabin kuma sun jikkata sosai.

Baya ga raunata kafaɗarta, ta kuma samu rauni a kai, amma an sallame ta daga asibiti bayan samun taimakon farko.

Amma bayan ‘yan kwanaki, bayan ta fara jin ciwon kai mai tsanani, aka yi mata ɗaukar hoton ƙwaƙwalwa wanda ya gano ƙaramin yanka daga bam a kan nata.

“Ina jin ciwo sosai wanda sai na sha magungunan rage zafi da dama nake jin sauƙi,” in ji ta.

Related Articles

3 Comments

  1. Hello http://viralkannywood.com,

    I design modern, user-friendly websites for small businesses and help improve their online presence.

    I wanted to check if you’re considering any updates to your current website—such as improving the design, usability, or adding features to better support your business.

    If you’re planning a new website or a redesign, feel free to share your requirements and reference website link.

    I’d be happy to discuss.

    Kind regards,
    Deepak Parcha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button