News
Trending

Viral Kannywood – Rikici na dada barkewa a jami’yyar APC a Kano

Wani taron hada kan jam’iyyar APC da aka gudanar a jihar Kano a jiya ya bar baya da ƙura.

An gudanar da taron ne da shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Nentawe Yilwatda da gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da kuma manyan jiga-jigar jam’iyyar na jihar, inda aka tattauna abubuwa da dama.

A wajen taron ne shugaban jam’iyyar na ƙasa ya tabbatar da cewa, “za a yi aiki da tsarin rabon shugabanci kashi 60 da kashi 40,” inda ya ce rabon zai kasance tsakanin sababbin masu shigowa jam’iyyar da kuma waɗanda aka tarar tun farko.

Bayan haka ne wani bidiyo ya bazu a shafukan sada zumunta inda aka ga Alhassan Ado Doguwa cikin fushi yana cewa Sanata Kawu Sumaila da Abdullahi Tijjaniya Muhammad Gwarzo “ba za su juya siyasar Doguwa da Tudun Wada yadda suke so ba.”

Na baya-bayan nan shi ne wanda ya ta so bayan wani zama da jiga-jigan jam’iyyar suka yi da gwamnan Abba kwana guda kafin a ba shi tutar jam’iyyar.

Bayan kammala taron mikawa gwamnan tutar jam’iyyar APC sai ga Sanata Kawu a wani bidiyo yana bai wa Hon Doguwa shawara a wani salon jirwaye mai kamar wanka. ‎

Masu lura sun ce wannan musayar saƙonni ta bidiyo na nuna cewa har yanzu rikicin bai lafa ba.

Masu sharhin siyasa na cewa siyasar Kano, wadda ake yi wa lakabi da “siyasar Kano sai Kano,” na iya shiga mawuyacin hali idan shugabannin jam’iyyar ba su haɗa kai ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button