News
Trending
Viral Kannywood – A rana irin ta yau a 13, ga shekaran 1976 aka kashe janar Murtala Mohammed

Yau ne tsohon shugaban mulkin soji na Najeriya, Murtala Mohammed ke cika shekara 50 da rasuwa.
A ranar 13 ga watan Fabarairun 1976, wasu matasan hafsoshin tsaron Najeriya da suka kira kansu “masu son kawo canji” suka sanar da kifar da gwamnatin Murtala.
Jagoransu, Bukar Suka Dimka wanda a lokacin yake da muƙamin laftanar kanal ne ya harbe shugaban ƙasa na lokacin, Murtala Muhammad a lokacin da yake tafiya a cikin mota.
Albarkacin wannan rana mun kawo muku wata wasiƙa da muka samu daga wani marubuci, Mohammed Bala Garba Maiduguri, ya turo, lokacin yana karatu a Jami’ar Maiduguri.




