
Wata gagarumar gobara na ci gaba da ƙone ɗaruruwan shaguna a kasuwar Singer da ke birnin Kano.
Gobarar wacce ta tashi da misalin ƙarfe bakwai na yammacin Asabar ta kai har zuwan misalin ƙarfe goma na dare tana ci gaba da ƙone shaguna, inda take yaɗuwa zuwa sassan kasuwar. Motocin kashe gobara da al’umma na ci gaba da yunƙurin kashe wutar.
Gobarar na zuwa ne ƙasa da mako biyu bayan wata gobara ta yi mummunan ta’adi a kasuwar. Kasuwar Singer ita ce kasuwar kayan masarufi mafi girma a arewacin Nijeriya.




