Viral Kannywood – Abin da ya sa na ƙi bin jami’an tsaron da suka so su kama ni – El-Rufai

Tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai ya ce babu wani nau’in bita da ƙulli da zai hana shi ci gaba da adawa da gwamnatin Najeriya, wadda ya ce ta jefa al’ummar ƙasar cikin mummunan yanayin da dole a tashi domin yaƙi da shi.
A ranar Alhamis 12 ga watan Faburairun 2026 jami’na tsaron Najeriya suka yi yunƙurin kama tsohon gwamnan jihar Kaduna, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja babban birnin Najeriya, jim kaɗan bayan saukar sa a Najeriya daga ƙasar Masar lamarin da ya janyo sa-in-sa a tsakanin su.
A hirar shi ta farko da BBC bayan dambarwar, Nasir El-Rufai ya yi bayanin abin da ya faru lokacin da jami’an tsaro suka yi yunƙurin kama shi.
Ya ce jayayyar ta taso ne lokacin da jami’an tsaron suka nemi ya bi su zuwa ofishin su domin ”ana son ganin shi” a can, shi kuma ya nemi su nuna mashi takardar gayyata a hukumance, lamarin da kuma ya ci tura saboda babu takardar a tare da su.




