News
Trending

Tinubu ya nemi a ƙara yawan alƙalan Kotunan Ɗaukaka Ƙara da na Tarayya a Nijeriya

Shugaba Tinubu ya kuma gabatar da wani kudiri da ke neman gyara Dokar Babbar Kotun Tarayya don ƙara yawan alkalai daga 70 zuwa 90, daga tanadin farko na 50.

 

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya aika da buƙatu da dama na gyara a fannin shari’ar ƙasar ga Majalisar Dattawa, inda shugaban ya nemi a ƙara yawan alkalai a manyan kotuna a faɗin ƙasar.

 

A yayin zaman majalisar na ranar Talata, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya karanta wata wasiƙa daga Shugaba Tinubu wadda ta nemi a yi wa Dokar Ɗaukaka Ƙara kwaskwarima don ƙara yawan alkalai daga 70 zuwa 110.

 

Shugaban ya ce matakin yana da nufin ƙarfafa ayyukan kotunan da kuma rage yawan shari’o’in da ake samu.

 

Kazalika Shugaba Tinubu ya kuma gabatar da wani ƙudiri da ke neman gyara Dokar Babban Kotun Tarayya don ƙara yawan alkalai daga 70 zuwa 90, daga tanadin farko na 50.

 

Sannan shugaban ya roƙi Majalisar da ta gaggauta yin la’akari da ƙudurorin da aka gabatar wadda aka aika zuwa ga Kwamitin Dokoki da Kasuwanci na Majalisar Dattawa don nazari da kuma ɗaukar matakin doka ta gaba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button