News
Trending

Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun samu wasu jami'an soji da laifin kisat juyin mulki a ƙasar a shekarar da ta gabata. Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce ta samu wasu ƙananan hafsoshi 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu cikin watan Oktoban 2025. Cikin watan Oktoban ne rundunar sojin ƙasar ta kama sojojin tare da ƙaddamar da bincike a kan su bayan zarginsu da rashin ladabi da saɓa wa dokokin aikin soji. Shalkwatar tsaron ƙasar ta ce a yanzu an kammala binciken, inda da dama cikin sojojin da aka tsaren suka tabbatar da yunƙurin juyin mulkin, wani abu da rundunar sojin ƙasar ta ce ya saɓa wa ƙa'idojin aikin soji da kundin tsarin mulkin Najeriya. Rundunar sojin ƙasar ta ce nan gaba za a gurfanar da jami'an gaban kotun soji don yi musu hukunci. A shekarun baya-bayan an riƙa samun zarge-zargen yunkurin juyin mulki a Najeriya, sakamakon tashe-tashen hankulu da rigingimu da matsin rayuwa, zargin da sojojin suka sha musantawa. Najeriya ta fuskanci juyin mulki masu yawa - tun bayan samun ƴancin kan ƙasar - a tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993. Sai dai tun bayan da ƙasar ta koma mukin dimokraɗiyya a 1999, sojojin ƙasar suka ɗauki batun yunƙurin juyin mulki ta matuƙar muhimmanci.

Hukumomin tsaron Najeriya sun ce sun samu wasu jami’an soji da laifin kisat juyin mulki a ƙasar a shekarar da ta gabata.

Cikin wata sanarwa da shalkwatar tsaron ƙasar ta fitar, ta ce ta samu wasu ƙananan hafsoshi 16 da laifin yunƙurin kifar da gwamnatin shugaba Tinubu cikin watan Oktoban 2025.

Cikin watan Oktoban ne rundunar sojin ƙasar ta kama sojojin tare da ƙaddamar da bincike a kan su bayan zarginsu da rashin ladabi da saɓa wa dokokin aikin soji.

Shalkwatar tsaron ƙasar ta ce a yanzu an kammala binciken, inda da dama cikin sojojin da aka tsaren suka tabbatar da yunƙurin juyin mulkin, wani abu da rundunar sojin ƙasar ta ce ya saɓa wa ƙa’idojin aikin soji da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Rundunar sojin ƙasar ta ce nan gaba za a gurfanar da jami’an gaban kotun soji don yi musu hukunci.

A shekarun baya-bayan an riƙa samun zarge-zargen yunkurin juyin mulki a Najeriya, sakamakon tashe-tashen hankulu da rigingimu da matsin rayuwa, zargin da sojojin suka sha musantawa.

Najeriya ta fuskanci juyin mulki masu yawa – tun bayan samun ƴancin kan ƙasar – a tsakanin shekarun 1966 zuwa 1993.

Sai dai tun bayan da ƙasar ta koma mukin dimokraɗiyya a 1999, sojojin ƙasar suka ɗauki batun yunƙurin juyin mulki ta matuƙar muhimmanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button