News
Trending
'Tinubu na cikin koshin lafiya bayan tuntuɓe a Turkiyya'
Shugaban Najeriya Bola Tinubu "na cikin koshin lafiya" bayan tuntuɓen da ya yi lokacin da ya ziyarci fadar shugaban Turkiyya a yau Talata, kamar yadda mai taimakawa shugaban kan harkokin yaɗa labarai, Suday Dare ya bayyana. Tinubu mai shekara 73, ya samu gagarumar tarba daga takwaransa na Turkiyya a wani biki da ya halarta an Ankara, babban birnin ƙasar. Wani bidiyo da aka wallafa a shafin X na shugaban Turkiyya, ya nuna lokacin da Tinubu ya yi tuntuɓe ya yi ƙasa sannan aka yi gaggawar kai masa ɗauki bayan wuce jerin sojoji da manyan baki da ke tsaye. Daga bisani aka haska Tinubu da Erdogan suna tattaunnawa. Babu wani rauni da shugaban Najeriyar ya samu bayan tuntuɓen, a cewar Suday Dare. An yi ta yaɗa hotunan bidiyo na tuntuɓen da shugaban ƙasar Najeriyar ya yi a shafukan sada zumunta.





