Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai kuma jigo a jam’iyyar hamayya ta ADC ya yi zargin cewa dole ne ta sa wasu yan siyasa ke sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC mai mulki ko kuma a ci gaba da zama a cikinta.
A wata tattaunawa da BBC, El-Rufa’i ya ce duk da cewa ba a riga an kama shi ba, an kama na kusa da shi, kuma yana tunanin za a iya zuwa kansa nan ba da daɗewa ba.
Tsohon gwamnan ya yin wannan zargi ne yayin da hada-hadar siyasa ke neman ɗaukar harama gabanin babban zaɓen ƙasar na shekara ta 2027.




