
Batun zargin Shugaban Najeriya Bola Tinubu da yunƙurin mayar da Najeriya mai bin tarfarkin jam’iyyar guda ya sake tasowa tun bayan da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya sanar da komawa APC.
A makon da ya gabata ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyarsa ta NNPP da aka zaɓe shi a cikinta a 2023.
Abba Kabir ya kasance gwamna na bakwai da ya koma APC bayan zaɓarsa a wata jam’iyya a 2023.
Baya ga gwamnonin, jam’iyyar APC ta kuma samu gagarumin rinjaye a majalisun dokokin ƙasar, sakamakon sauya sheƙa da wasu mambobin majalisar suka yi zuwa jam’iyyar mai mulki.



