
Nan gaba a yau ne gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf zai sanar da komawa jam’iyyar APC a hukumance bayan raba gari da ubangidansa a siyawa, Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda shi ne jagoran jam’iyyar NNPP.
A ranar Juma’a ne Abba Kabir ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar NNPP da aka zaɓe shi a karkashinta a shekarar 2023.
Gwamnan ya bayyana rikicin cikin gida da fifita ci gaban al’ummar jihar Kano a matsayin dalilansa na ficewa daga NNPP.
Tuni dai jam’iyyar ta yi masa martani, cikin wata sanarwa da ta fitar, inda ta bayyana matakin a matsayin rashin mutunta masu kaɗa ƙuri’ar da suka ba shi gagarumin goyon baya a zaɓen gwamna na 2023.




