
Gwamnatin Iran ta tabbatar da mutuwar Ayatollah Khamenei, bayan ikirarin farko da shugaba Donald Trump ya yi na kisan jagoran addinin a hare-haren da Amurka da Isra’ila suka kai a sassan kasar Iran.
A sanarwar da kafar yada labaran Iran ta sanar, ba a bayyana yadda aka kashe jagoran addinin ba da kuma wanda zai gaje shi.
Majalisar koli ta tsaron kasar Iran ce ta tabbatar da mutuwar Khamenei tana mai zargin Amurka da Isra’ila, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ce shahadar Khamenei za ta kasance mafarin “yaki da azzalumai”.




