News
Trending

Iran ta gargaɗi ƙasashen Gabas ta Tsakiya kan 'tallafa wa Amurka'

Iran ta ce za ta yi amfani da duka karfin sojinta wajen kare kanta daga hare-haren Amurka da Isra’ila.

Cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen ƙasar, Abbas Araghchi ya fitar ya ce ya yi waya da ƙasashen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa da Qatar da Kuwait da Bahrain da Iraƙi, inda ya shaida musu cewa Iran za ta yi amfani da duka karfin sojinta wajen kare kanta.

Araghchi ya kuma “tunasar da” ƙasashen game da “damarsu ta hana amfani da kayayyakinsu ko yankunansu ta hanyar da ba ta dace ba” yana nufin kada su bai wa Amurka ko Isra’ila damar amfani da su don ƙaddamar da hari cikin Iran.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button