News
Trending

Viral Kannywood – Kotu ta yanke wa Samha hukuncin ɗaurin wata shida

Babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta yanke wa jarumar fina-finan Kannywood Samha M Inuwa hukuncin ɗaurin wata shida saboda samunta da laifin wulakanta naira.

Makonni biyu da suka gabata ne jami’an hukumar EFCC, mai yaƙi da almundahanar kuɗi a Najeriya ta suka kama jarumar bayan ɓullar wani bidiyo da a ciki take face majina da takardar naira 1,000.

Jaridar Daily Nigerian ta ce an gurfanar da matashiyar jarumar a gaban kotu bisa zargin, wanda EFCC ta ce ya saɓa wa sashe na 21 na dokar CBN ta 2007.

Samha M Inuwa ta amsa lafin da ake zarginta da shi, tare neman sassauci daga kotun, tana mai cewa wannan ne karon farko da aka sameta da laifi.

Daga nan ne kuma alƙalin kotun, Maishari’a M.S Shuaibu ya yanke mata hukuncin ɗaurin wata shida a gidan yari tare da zaɓin biyan tarar naira 200,000.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button