
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi kira ga Musulmi da Kiristoci su ƙarfafa haɗin kai yayin da lokutan azumin Ramadan da na Kirista wato Lent suka zo a lokaci guda a bana, yana mai cewa hakan wata dama ce ta ƙarfafa zumunci tsakanin mabiya addinai.
A cikin sanarwar da fadar shugaban ƙasa ta fitar, Tinubu ya bayyana cewa ba kasafai ake samun haɗuwar lokutan ibadar biyu ba, kuma hakan na tunatar da ƴan Najeriya cewa “su al’umma ɗaya ce a wurin ubangiji duk da bambancin addinai”.
Ya ce “ga Kiristoci, lokacin azumi lokaci ne na tuba da kuma koyi da misalin sadaukarwa, yayin da ga Musulmi kuma Ramadan watan ibada ne mai daraja da ke nuna biyayya ga Allah ta hanyar sadaukarwa da ibada da hidima da taimakon juna.”
Shugaban ya buƙaci al’ummar Najeriya “su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai da kwanciyar hankali, tare da yi wa ƙasa addu’ar samun ci gaba da tsaro.”
Ya kuma ja hankalin jama’a su rayu bisa kyawawan koyarwar addinansu.




