News
Trending

Ci gaba da girke dakarun Amurka a Gabas ta Tsakiya na ƙara nuna yadda Amurkar ke shirin far wa Iran.

Isar jirgin ruwan yaƙin Amurka USS Abraham Lincoln kusa da gabar ruwan Iran, shi kaɗai wani babban mataki ne.

An kuma ga wani jirgin ruwan yaƙi USS Gerald R Ford kusa da mashigar Gibraltar inda ya nufi gabashi domin taimakawa. Har ila yau an kuma kai wasu kayan yaki zuwa yankin, abin da ke nuni da cewa Washigton na duba yiwuwar ɗaukar matakin soja.

Aika irin waɗannan abubuwa na nuna cewa ba a ɗauki hanyar diflomasiyya ba. Hakan kuma na iya nuna cewa ba a cimma matsaya ba a tattaunawar kai-tsaye tsakanin Tehran da Washington – abin da zai sa a ɗauki matakin soji idan kowane ɓangare ya ja daga.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button