News
Trending
Tsananin sanyi ya yi ajalin aƙalla mutum 20 a Amurka
Tsananin sanyi ya yi ajalin aƙalla mutum 20 a Amurka

Akalla mutane 20 sun mutu sakamakon tsananin sanyi da zubar dusar kankarar da ake fama da su a jihohin kudanci da kuma gabashin Amurka.
Tsananin Sanyin ya sa wutar lantarki ta dauke inda mutane da dama ke zama ba tare da hasken lantarki ba.
Kazalika tsananin sanyin ya janyo soke tashi da saukar jiragen sama a kasar.
Jihohi 20 sun ayyana dokar ta baci yayin da a wasu yankunan Canada ciki har da Toronto kuma ake fama da zubar dusar kankara.




