News
Trending

Sojoji sun shirya kirar da Gwamnatin TINUBU a satin ban 2025

TABBAS ALLAH YA KIYAYE FARUWAR MUMMUNAN LAMARI A NIGERIA

Yadda hukumar DSS da Shugaban rundinonin Sojin Nigeria CDS Oloyede suka dakile shirin kash£ Shugaban Kasa Tinubu da wasu mutane kamar yadda jaridar Premium Times ta tattara bayanan ta ruwaito

Wani sirrin aikin tattara bayanan leken asiri da Hedkwatar Sojoji da Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) suka jagoranta ne ya taimaka wajen dakile wani mummunan shiri na kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu tare da kashe manyan ’yan siyasa, kamar yadda PREMIUM TIMES ta tabbatar

Wasu manyan jami’an gwamnati sun ce shirin ya fara ne a ƙarshen watan Satumba 2025, bayan wani jami’in soja (wanda ba a bayyana sunansa ba) da ke da cikakken masaniya kan shirin juyin mulkin ya tuntubi shugaban sojoji na wancan lokaci, Olufemi Oluyede

An ruwaito cewa jami’in ya bayyana shirin ne saboda tsoron kada a danganta shi da laifin cin amanar kasa idan bai sanar da hukumomi ba

Majiyoyin Premium Timed sun ce a daidai wannan lokaci, SSS ma ta tattara bayanan sirri da ke nuna cewa wasu sojojin da ke aiki suna shirin “tayar da zaune tsaye da lalata dimokuraɗiyyar Nijeriya”

Wani jami’i da ke da masaniya kan lamarin ya ce Darakta Janar na DSS, Oluwatosin Ajayi, ya je da kansa ya sanar da Mista Oluyede sakamakon binciken

Da yake fuskantar bayanai daga bangarori daban-daban, shugabannin tsaron biyu suka yanke shawarar daukar mataki cikin gaggawa

Aka kaddamar da wani hadin gwiwar aiki mai fadi amma a asirce tsakanin sojoji da DSS, inda aka tsara kama mutane a sassa daban-daban na Kasar domin kawar da masu jagorantar juyin mulkin da sauran masu hannu a ciki

A ranar 30 ga Satumba 2025, yayin da Shugaba Tinubu ke tafiya zuwa Jihar Imo domin ziyarar aiki ba tare da sanin shirin kifar da shi ko yi masa kisan gilla ba aka fara aiwatar da wannan aiki na hadin gwiwa

An kama wadanda ake zargi da kasancewa manyan masu shirya juyin mulkin tare da wasu sojoji da fararen hula

Daga bisani aka sanar da Shugaban Sashen Leken Asirin Tsaro na Soji (CDI) Emmanuel Undiandeye, da kuma Shugaban Rundunar Sojoji na wancan lokaci Janar Christopher Musa

Daga nan aka bukaci Mista Undiandeye ya tsare wadanda ake zargi a wani wurin tsarewa na karkashin kasa na Hukumar Leken Asirin Tsaro (DIA)
Bayan kamun farko, an sanar da Shugaba Tinubu a hukumance game da shirin da aka dakile

An ce Shugaban kasa Tinubu ya firgita kwarai, nan take ya bayar da umarnin soke bikin faretin ranar ’Yancin Kai ta 1 ga Oktoba 2025, Haka kuma ya amince da kafa wani kwamitin bincike na musamman, wanda daga baya ya haifar da karin kama wasu Sojoji da fararen hula, Janar Undiandeye ne ya jagoranci kwamitin

Daya daga cikin sojojin da aka tsare ya tsere, amma jami’an DSS suka sake kama shi a Bauchi in ji wani jami’in soja

A halin da ake ciki, wani tsohon jami’i mai suna Janar Adamu da kuma tsohon Gwamna, Timipre Sylva wadanda ake zargi da daukar nauyin masu shirin juyin mulkin suna Kasar waje, ba a kama su ba.

Daga baya Shugaban Kasa Tinubu ya kori Shugaban Rundunar Sojoji na wancan lokaci, Janar Musa, da kuma shugabannin rundunar ruwa da ta sama, Manjo Janar Oluyede aka nada a matsayin CDS tare da kara masa girma zuwa mukamin Janar

Duk da tarin hujjoji da jerin rahotanni masu zurfi daga PREMIUM TIMES da sauran kafafen yada labarai, sojoji sun rika musanta cewa akwai wani shirin juyin mulki

Sai dai a ranar 26 ga Janairun 2026, sojoji sun amince a karon farko a fili cewa jami’ai sun shirya kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu ta haramtacciyar hanya, sun sanar da cewa za a gurfanar da wadanda aka tuhume su a gaban kotun soja

A cewar Hedkwatar Tsaro, binciken ya kasance “cikakke” kuma an gudanar da shi bisa ka’idojin da aka tanada, inda aka duba “dukkan yanayin halayen jami’an da abin ya shafa.”
Ta ce sakamakon binciken ya gano “wasu jami’ai da ake zargi da shirin kifar da gwamnati,” inda ta bayyana irin wannan hali a matsayin “abin da ya sabawa ɗabi’u, kima da ka’idodin kwarewa da ake bukata daga mambobin Rundunar Sojin Nigeria

“Saboda haka, duk wadanda ke da abin amsawa za a gurfanar da su a gaban kotun soja da ta dace domin fuskantar shari’a bisa Dokar Rundunar Soji da sauran dokokin aiki,” in ji sanarwar

Shirin kifar da Tinubu da kashe shi da wasu jami’an Gwamnati
A wani rahoto na baya, PREMIUM TIMES ta nakalto majiyoyi masu cikakken sani kan binciken da suka bayyana manyan jami’an da ake zargin an saka su a jerin kisan gilla idan anyi juyin mulki wanda suka hada da Shugaban Kasa Tinubu, Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas duk anyi shirin kashe su

“Akwai wasu mutane ma da aka nufa,” in ji wata majiya. “Amma wadannan su ne manyan makasudin, masu shirin juyin mulkin sun kuma yi niyyar tsare manyan jami’an soja, ciki har da shugabannin rundunoni. “ amma ba su shirya kashe su ba,” in ji majiyar Premium Times

A cewar majiyoyin, makircin ya tanadi a kashe shugabannin siyasa a lokaci guda. “Suna jiran ranar da dukkaninsu za su kasance a Kasar,” in ji wani jami’i. “duk inda suke, za a kashe su.”

Majiyoyin sun ce masu shirin sun dogara da masu basu bayanai a cikin Fadar Shugaban Kasa da kuma kusa da jami’an da aka sa a gaba.
“Masu shirin juyin mulkin suna da mutane a cikin Villa da ke bibiyar motsin wadannan jami’ai,” in ji majiyar. “Shirin shi ne a kashe su lokaci guda sannan a kafa Gwamnatin soja.” Rahoton Premium Times

Ba shakka Allah Madaukakin Sarki ya kiyaye mana faruwar mummunan al’amarin da zai iya jefa Kasarmu Nigeria cikin yakin basasa inda Sojojin sun kai ga aiwatar da abinda sukayi niyya

Muna rokon Allah Ya kare mana Kasarmu Nigeria daga dukkan sharri da fitina da tashin hankali

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button