
Baya ga Abuja babban birnin Najeriya da ake gudanar da zaɓukan shugabannin ƙananan hukumomi, hukumar zaɓen na jagorantar zaɓukan cike gurbi a jihohin Kano da Rivers.
A jihar Kano da ke arewa maso yammacin ƙasar ana gudanar da zaɓukan ƴanmajalisun dokokin jihar na ƙananan hukumomin Munincipal da Ungogo.
Haka ma a jihar Rivers da ke kudu maso kudancin ƙasar, ana gudanar da zaɓukan cike gurbi na ƴanmajalisun dokokin jihar a gundumomin Ahoada East II da Khana II.
Tuni dai Shugaba Tinubu ya yi kira ga jami’an tsaro su tabbatar da doka a zaman lafiya a lokacin zaɓukan.



