News
Trending

Ana duba yiwuwar sanyawa wasu mutane takunkumi kan zargin muzgunawa kiristoci

Kwamitin majalisar wakilan Amurka ya gabatar da wani ƙudiri na neman ɗaukar mataki kan zargin musguna wa kiristoci da ayyukan wasu ƙungiyoyin ƴan bindiga a Najeriya.

Ƙudirin mai suna taken ‘Nigeria Religious Freedom and Accountability Act’ ya buƙaci Sakataren Harkokin Wajen Amurka ya riƙa gabatar wa kwamitocin harkokin wajen majalisa rahoto duk shekara kan kokarin magance musguna wa Kiristoci a Najeriya.

Haka kuma ƙudirin ya buƙaci a duba yiwuwar ayyana wasu kungiyoyin da ake dangantawa da “makiyaya Fulani a matsayin kungiyoyin ta’addanci na ƙasashen waje.”

Bugu da ƙari, ƙudirin ya kuma buƙaci a sanya takunkumi kan wasu mutanen da ake zargi suna da alaƙa da cusguna wa kiristoci.

Ana buƙatar ƙudirin ya samu amincewar majalisun dokoki biyu kafin ya zama doka.

Matakin na zuwa ne bayan Amurka ta sanar da shirin tura sojoji 200 zuwa Najeriya domin horas da sojojin ƙasar kan yaƙi da masu tayar da ƙayar baya.

Ana sa ran za su isa Najeriya cikin makonni masu zuwa, inda za su haɗu da wata ƙaramar tawaga da aka riga aka tura tun farko.

Kakakin rundunar sojin Najeriya, Janar Samaila Uba, ya tabbatar da batun ga BBC, yana cewa hakan ya biyo bayan gayyata da buƙatar gwamnatin Najeriya,  kuma ya dace da shawarwarin kwamitin hadin gwiwar Amurka da Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button