News
Trending

Amurka ta fara yunƙurin daidaita alakarta da ƙasashen Sahel

 

Ofishin kula da harkokin Afirka na Amurka ya ce babban jami’insa Nick Checker na kan hanyarsa ta zuwa ƙasar Mali domin ƙoƙarin daidaita alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

A cikin abin da ya bayyana a matsayin sanarwar sasantawa da aka wallafa a shafukan sada zumunta, ofishin ya bayyana sha’awar Washington na magance ‘rashin fahimta’ da aka samu a baya da niyyar inganta dagantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu.

Sanarwar ta ƙara da cewa, “Amurka na fatan tattaunawa kan matakai na gaba don inganta haɗin gwiwar Amurka da Mali da kuma tuntuɓar wasu gwamnatocin yankin, ciki har da Burkina Faso da Nijar, kan samun daidaito a batutuwan da suka shafi tsaro da tattalin arziki.”

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun ɓaraka a dangantakar da ke tsakanin ƙasashen yankin Sahel da ƙawayensu na yammacin duniya, musamman bayan wasu juyin mulkin da aka yi a ƙasashen.

Dangantakar ta ƙara tsami ne a lokacin da gwamnatocin mulkin sojan ƙasashen suka umurci sojojin ƙasashen yammacin duniya da suka hada da sojojin Amurka da na Faransa da su fice daga yankin Sahel duk da irin gudunmawar da suke bayarwa wajen yaƙi da ta’addanci a yankin.

Tuni dai suka ƙula alaƙa ta ƙut da ƙut da Rasha domin neman agajin soji da tsaro, lamarin da ya haifar da jibge sojojin haya da kuma kayan yaƙin rasha a yankin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button