News
Trending

Tsohon shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya koma APC a yau yanzu shi ne jagoran jam'iyyar a Kano. Yayin da yake jawabi a wajen taron bikin komawar gwamnan APC da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar, Ganduje ya ce jam'iyyar APC na maraba da shigar Abba tare da mutanensa zuwa APC. Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce kamar yadda tsarin jam'iyyar yake cewa gwamna shi ne jagoran jam'iyyar a kowace jiha ba. ''Don haka a nan ma yanzu kai ne jagoran jam'iyyar APC a jiharmu ta Kano'', in Ganduje.

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf da ya koma APC a yau yanzu shi ne jagoran jam’iyyar a Kano.

Yayin da yake jawabi a wajen taron bikin komawar gwamnan APC da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar, Ganduje ya ce jam’iyyar APC na maraba da shigar Abba tare da mutanensa zuwa APC.

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya ce kamar yadda tsarin jam’iyyar yake cewa gwamna shi ne jagoran jam’iyyar a kowace jiha ba.

”Don haka a nan ma yanzu kai ne jagoran jam’iyyar APC a jiharmu ta Kano”, in Ganduje.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button