News
Trending

Manyan cibiyoyi biyar da aka fi safarar bayi a Afirka

  • Lokacin karatu: Minti 6

Bauta da safarar bayi daga Afirka na cikin abubuwan da suke da muhimmanci a tarihin nahiyar, lamarin da ya sa wasu idan suka yi waiwaiye, suka duba abubuwan da suka faru, sukan shiga damuwa da tausayi.

A ƙididdigar Hukumar kula da al’adu da ilimi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), tsakanin mutane miliyan 15 zuwa miliyan 20 ne aka tursasa wa barin ƙasashensu, aka yi safararsu zuwa ƙasashen waje. Daga ciki akwai kusan miliyan 10.5 da suka isa yankin Amurka da Caribbean.

Wannan safarar da aka yi, ta taimaka wajen canja tarihin nahiyar da rusa masarautu, kamar yadda Maryse Condé ta wallafa a littafinta mai sun “Segou,” wanda a ciki ta bayyana yanayin kasuwancin bayi a Afirka ta Yamma.

Duk da haramta cinikayyar bayi da aka yi a hukumance, har yanzu akwai alamu da gurabun harkar da ake iya ci gaba da gani ana tuna baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button