Hukumomin asibitin Alert da ke Hukumomin asibitin Alert da ke Habasha sun sanar da kammala aikin mayar wa wani matashi mazakutarsa da ta guntule bayan tiyatar sa’a bakwai da aka yi masa.
Shugaban sashen tiyata na asibitin, Dr. Abdirisaq Ali ya shaida wa BBC cewa matashin ya ji raunin ne ranar Asabar, inda aka kai shi asibitin da daddare.
”Da safiyar ranar Lahadi aka kira ni daga asibitin ana tambayar ko za a iya mayar masa da guntulalliyar mazakutar tasa,” in ji shi.
“Bayan auna raunin, mun yanke shawarar yi masa aiki domin sake mayar da ita, ganin cewa za ta iya ci gaba da aiki, kasancewar ba a ɗauki lokaci da jin raunin ba aka garzaya da shi asibitin,” kamar yadda ya yi ƙarin haske.
sun sanar da kammala aikin mayar wa wani matashi mazakutarsa da ta guntule bayan tiyatar sa’a bakwai da aka yi masa.