News
Trending

Kotu ta yi watsi da buƙatar Kanu na a sauya masa gidan yari

Kotun ƙolin tarayya da ke Abuja ƙarƙashin jagorancin Maishari’a James Omotosho ta yi watsi da buƙatar shugaban ƙungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da ya shigar na neman ɗauke shi daga gidan yarin Sokoto.

A zaman kotu da aka yi a ranar Talata, alkalin ya ce, “A ranar 8 ga Disamba na uamrace ka da ka sanar da waɗanda shari’ar ta shafa, wato gwamnatin tarayya da hukumar gyaran hali game da wannan buƙata taka”.

“Amma daga bisani, babu wata shaida da ta nuna cewa an aiwatar da wannan umarni ko cewa an sanar da su yadda ya dace.”

Saboda haka ne alƙalin ya ce shari’ar Nnamdi Kanu ba ta da inganci wanda ya sa yayi watsi da ita.

A zaman kotun ne lauya mai wakiltar Kanu, Demdoo Asan ya shaida wa kotu cewa yana so ya janye daga shari’ar, yana mai cewa akwai rashin jituwa da ba za a iya warwarewa ba.

Demdoo ya kara da cewa Kanu yana son ya tsara abin da lauya zai fada a gaban kotu, wanda ya ce a matsayin jami’in kotu ba zai iya amincewa da hakan ba.

A hukuncinsa, alƙali Omotosho ya amince da buƙatar lauyan na ya janye daga kare Kanu inda ya yaba wa lauyan saboda kiyaye darajar kotu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button