
Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf ya koma jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya, amma da yawan mutane na ta tambayar, shin mene ne haƙiƙanin dalilinsa na barin tafiyar Kwankwasiyya?
Raba gari da Kwankwaso da Abba ya yi ya bai wa mutane da dama mamaki, kasancewar yana cikin wadanda ake yi wa kallon ‘yan amanar tafiyar Kwankwasiyya.
Kafin ranar Alhamis 22 ga watan nan, wasu jami’an gwamnatin Kano a wani ƙoƙarin ƙarshe na ganin an ci gaba da tafiya a dunƙule, sun yi ta yunƙurin ganin Kwankwaso ya shiga tafiyar ta komawa APC, sai dai da alama roƙon bai karɓu ba.
Sanarwar Abba Kabir Yusuf ta ce gwamnan ya bar inuwar Kwankwaso ne saboda rikicin cikin gida da ya yi wa NNPP katutu da kuma muradin ci gaban Kano.




