News
Trending

Dalilin da yasa na koma APC - AKY

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kammala komawa jam’iyyar APC a hukumance.

An gudanar da taron komawar gwamnan a wani ƙwarya-ƙwaryan biki da aka shirya a gidan gwamnatin jihar.

Taron ya samu halartar tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da mataimakin shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Barau Jibrin da Sanata Kawu Sumaila da Shugaban jam’iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas da ƙaramin ministan gidaje Abdullahi Ata da sauran manyan baƙi.

Yayin da yake jawabi a wajen taron gwamnan ya ce ya ɗauki matakin komawa jam’iyyar APC bayan tuntuɓar abokansa na siyasa, da kuma ci gaban al’ummar jihar Kano.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button