News
Trending

Najeriya ta gargadi yan kasar dake zaune a Iran da kasashen larabawa

– Gwamnatin Tarayyar Nijeriya tana sa ido sosai kan halin da ake ciki a Gabas ta Tsakiya, bayan matakan soja da Isra’ila da Amurka suka ɗauka kan Iran, da kuma hare-haren ramuwar gayya da Iran ta kai kan wasu wurare a wasu kasashen yankin Gulf.

– An shawarci ’yan Nijeriya da ke Iran da ƙasashen Gulf da ke makwabta su kasance cikin shiri da taka-tsantsan, su guji wuraren soji ko na gwamnati, kuma su rika kula da abin da ke faruwa a kewaye da su a kowane lokaci.

– An bukaci ’yan Nijeriya su rage zirga-zirga da tafiye-tafiye marasa muhimmanci, su kuma guji tarurruka masu yawa, har sai yanayin tsaro ya daidaita.

– An shawarci ’yan ƙasa su bi umarnin hukumomin ƙasashen da suke ciki, su kuma rika samun labarai daga sahihan kafofi, tare da guje wa jita-jita da labaran ƙarya.

– Ofisoshin jakadancin Nijeriya da ke Tehran, Qatar, Bahrain, Kuwait, Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da Saudiyya suna cikin shirin ko-ta-kwana, domin ba da taimako, kuma Gwamnatin Nijeriya ta jaddada cewa kare lafiyar ’yan Nijeriya a ƙasashen waje shi ne babban abin da ta fi ba muhimmanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button