
Tsohon gwamnan Jihar Kaduna da ke Nijeriya, Mallam Nasir El-Rufai, yana hannun hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa, a cewar mai magana da yawunsa Muyiwa Adekeye.
A saƙon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis da safe, Adekeye ya ce tsohon gwamnan ya bar hukumar EFCC mai yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin Nijeriya ta’annati inda ya kai kansa ranar Litinin ɗin da ta wuce.
Bai yi ƙarin bayani kan laifukan da ICPC take zargin El-Rufai da aikatawa ba, sai dai a baya tsohon gwamnan ya yi zargin cewa gwamnatin Nijeriya tana yin amfani da hukumar domin yi masa bi-ta-da-ƙulli.



