
Da ɗumi-ɗumi: Amurka ta kakaba wa Kwankwaso takunkumi da wasu ‘yan Najeriya 8 kan alaƙa da Boko Haram da laifukan yanar gizo
Gwamnatin Amurka ta sanar da kakaba takunkumi ga wasu ‘yan Najeriya takwas bisa zargin alaƙa da ƙungiyoyin ta’addanci da kuma aikata laifukan yanar gizo.
Hukumar kula da kadarori ta Ma’aikatar Kuɗin Amurka (OFAC) ta ce matakin ya haɗa da kulle dukiyoyinsu da hana duk wata mu’amala da su a cikin ƙasar Amurka.
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin mutanen akwai tsohon gwamnan jihar Kano sen Rabi’u Musa Kwankwaso da waɗanda ake zargi da taimaka wa ƙungiyar Boko Haram da ISIL ta fuskar kuɗi, yayin da wasu kuma ake danganta su da manyan laifukan damfara ta yanar gizo.
Amurka ta ce wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinta na dakile hanyoyin samun kuɗaɗen ta’addanci da kuma yaƙi da laifukan intanet da ke barazana ga tsaro a duniya.




