News
Trending

El-Rufai ya zargi ofishin Ribadu da safarar guba ‘mai haɗari’

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya zargi ofishin mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, a ƙaƙashin jagorancin Mallam Nuhu Ribadu, da sayo kimanin kilogiram 10 na wani sinadari mai haɗari da ake kira ‘thallium sulphate’, daga ƙasar Poland.

El-Rufai ya yi wannan zargin ne a cikin wata wasiƙa da ya aike wa ofishin Ribadu, wadda kuma ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce jagororin adawar ƙasar na neman ƙarin haske game da wannan batun.

“Sinadarin thallium na da matuƙar haɗari kuma sinadari ne da ba kasafai ake samunsa ba”, kamar yadda wasiƙar El-Rufai ya bayyana cikin wasiƙar tasa.

Ya ce ya aike da wasiƙar ne domin ya nemi cikakkun bayanai kan yadda aka sayo sinadarin, yayin da ya nuna barazanar da irin wannan sinadari ka iya yi kan lafiyar al’umma.

El-Rufai ya nemi dalilin shigo da sinadarin da kuma amfanin da za a yi da shi.

“Ina so in jaddada cewa ba ni da wata manufa ta daban na yin waɗannan tambayoyi, na yi su ne don in tabbatar da cewa an bi tsarin da ya kamata, kuma an bi matakan da suka dace na kare lafiya.”in ji shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button