News
Trending

Viral Kannywood – Abin da majalisar dokokin Amurka ta ce a kan Kwankwaso da Miyetti Allah

Ƴan majalisar wakilan Amurka sun gabatar da wani ƙuduri a zauren majalisar wanda ya ƙunshi rahoto kan kwamitin bincike game da zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Najeriya.

Haka nan rahoton ya bayar da shawarwari kan matakan da suka kamata Amurkar ta ɗauka wajen magance matsalar.

Wasu ƴan majalisa na jam’iyyar Republican ne suka gabatar da ƙudurin, wanda a ciki suke kira ga sakataren harkokin wajen Amurka kan ya ayyana wasu ƙungiyoyi ƴan bindiga a matsayin ƴan ta’adda, sannan kuma a sanya takunkumi kan wasu ƴan Najeriya.

Sauran matakan da ƙudurin ke son a ɗauka su ne hana waɗanda ake zargi da hannu a ‘cin zarafin’ kiristoci shiga Amurka da riƙe kadarorinsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button