
Bayanai sun ce jami’an tsaro a filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, babban birnin Najeriya sun ƙwace takardar tafiye-tafiyen tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufa’i, jim kaɗan bayan saukar sa a Najeriya daga ƙasar Masar.
Sanarwar da mai taimaka wa tsohon gwamnan kan yada labarai Muyiwa Adekeye ya wallafa a shafinsa na X, ta ce “A yau jami’an tsaro sun so su kama Nasir El-Rufai bayan komawarsa gida daga birnin Cairo.
Ya ci gaba da cewa “El-Rafai ya ƙi bin su ba tare da an nuna masa takardar gayyata ba a hukumance, sai dai duk da haka sun ƙwace takardar fasfo dinsa daga hannun wani mai taimaka masa.”
Wani bidiyo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda tsohon gwamnan ke magana da wasu mutane a filin jirgin, inda yake cewa “idan kuna son ku gayyace ni ku ba ni takardar gayyata.”
Nasir El-Rufai wanda tsohon gwamnan jihar Kaduna ne na cikin jagororin adawa a Najeriya wadanda suka dunƙule a jam’iyyar ADC domin ƙalubalantar shugaba mai ci Bola Tinubu a babban zaɓen ƙasar da za a yi a shekara mai zuwa.
Cikin makon, a wata tattaunawa da BBC, El-Rufai ya zargi gwamnatin jam’iyyar APC da yi wa ƴan adawar da suka ƙi sauya sheƙa zuwa jam’iyyar barazana ta hanyar kama su da sunan bincike kan ayyukan rashawa.
“An kama mutum wajen guda huɗu waɗanda muka yi aiki da su a Kaduna, saboda haka ni ma lokaci ne, ni ma za a neme ni,” in ji El-Rufa’i a tattaunawar tasa da BBC.



